News

Yadda Ta Kashe Mijin Kawarta Bayan Ya Kamasu Suna Madigo Akan Gadonsa

Wata mata da ake zargi ƴar maɗigo ce ta kashe mijin abokiyar ta da wuka a kauyen Onitsha dake karamar hukumar Ontisha ta Kudu a jihar Anambra.

Wannan mummunar abu ya auku ranar Talatar makon jiya da misalin karfe 9:20 na dare.

Magidancin da aka kashe mai suna Ikechukwu Onuma ma’aikacin kwalejin kiwon lafiya ne dake Onitsha sannan ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da ya dawo gida ya iske matarsa da ƙawarta kwance kan gado suna aikata maɗigo.

Matar mamacin Nkemdili ta tsere a lokacin da ta ga mijinta ya yanke jiki ya faɗi kasa muce bayan ƙawarta ta daɓa masa wuka.

Mutane sun ce marigayi Onuma bai san cewa matarsa Nkemdili ta dade tana buga irin wannan harka da mata ba.

Kakakin rundunar Tochukwu Ikenga ya tabbatar da kisan sannan ya ce rundunar ta kama Ebele Onochie yanzu tana tsare a ofishinsu.

Ikenga ya ce kwamishinan ‘yan sanda ya bada umurnin Kai karan zuwa ga fannin dake gurfanar da masu aikata laifi irin hakq domin gudanar da bincike.

“Onuma ya rasu a lokacin da likita ke duba shi a asibiti.

Zuwa yanzu ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike akai.

Dokar hana liwadi da madigo a Najeriya.

A shekarar 2014 ne gwamnatin Najeriya ta saka dokar haramta luɗu da madigo a kasar nan.

Bisa ga dokan hukuncin duk wanda aka kama yana
ko rana aikata haka za a ɗaure shi na tsawon shekara 14.

Yadda Ake Amfani da Aloe Vera Wajen Gyaran Fata

Mata da dama na sha’awar ganin fatarsu ta yi sumul babu ƙuraje ko kaɗan. Wannan ganyen yana ɗauke ne da sinadarai da dama waɗanda sukan iya dada tsawon gashin mace, sanya fuska sheƙi, gyaran jiki da dai sauransu.

Saboda haka ne a yau na kawo muku hanyoyin da za’a bi domin amfani da ganyen wajen gyaran fata da kuma gashin kai. Inaso masu karatu su gane cewa a duk rubutun da nake yi, idan na lissafo ababen hadin kwalliya, guda ɗaya daga ciki nake so a rika amfani dashi.

Domin yawan sanya wa fuska ababe da dama na haifar da fesowar ƙuraje.

ABUBUWA DA ALOE VERA KEYI:

1. Koɗewar fuska: yawan aiki ko shiga rana na sanya fuska ta yi baƙi ko kuma launinta ya zama biyu. A sami ganyen ‘aloe bera’ sannan a matse ruwan sai a matsa ruwan lemun tsami sannan a kwaba a rika shafawa a fuska domin gyaran irin wannan fatar.

2. Yanƙwashewar fata: wannan ganye na rage shekaru daga fuskar mutum. A matso ruwan sa sannan a haɗa da ruwar ‘rose’ sai a rika shafawa a fuska a bari na tsawon minti goma zuwa goma sha biyar kafin a wanke a kullum.

3. Domin fuska mai yawan gumi/maiko: a sami ganyen sai a dan kankare bayansa sannan a ɗora a tukunya da ruwa har sai ya yi laushi sannan a sauke a zuba zuma bayan ya huce sannan a shafa a fuska na tsawon minti 20 a kullum kafin a shiga wanka.

4. Domin gautsin fata: a markaɗa dabino da gurji sannan a matsa ruwan ganyen ‘aloe vera’ da ruwan lemun tsami sannan a shafa a fuska da jiki na tsawon minti talatin kafin a wanke.

5. Gyaran gashi: a matse ruwan ‘aloe bera’ sannan a haɗa da man zaitun a kwaɓa su kwaɓu sosai sannan a riƙa shafawa a fatar kai da kuma saman gashin a duk lokacin da aka yi niyyar wanke gashin kai kafin a wanke . Yin hakan na sanya baƙin gashi da kuma daɗa wa gashin tsawo da ƙarfi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button