Wasu Mazan Sai A Hankali! Mijina Yana Saduwa Dani Kamar Daga Yau Shikenan Wata Mata Ta Kai Karar Mijinta
Duk da cewa rayuwar aure tana bukatar sirri amma wasu maginda sunkai kansu kotu inda suka tonawa kansu asiri.
Wani magidanci ya kai karan matansa wata kotu a garin Akure jihar Ondo bisa laifin aikata karuwanci da rashin yi masa da’a.
Ya fada wa kotun cewa matarsa na yawan sanya kanana tufafin da ke nuna tsiraicinta wanda hakan ke matukar bata masa rai duk da cewa ya yi kokarin hana ta amma ta ki.
Michael Adaramola ya ce idan har dai ya ci gaba da zama ta ita lalle zai kama cutar hawan jini wanda haka ne ya sa yake rokon kotu ta warware aurensu da ya ke shekara na tara Kenan.
Da take amsa lafinta Esther Adaramola wato matar Michael, ta amince a raba auren su domin yawan kwanciya da mijinta ke yi da ita.
Esther ta fada wa kotun cewa banda yawan kwanciya da ita da mijinta ke yi yana kuma hadawa da wasu kwayoyi wanda kan haukatar da shi a lokacin da suke saduwa.
Ta kuma nuwa wa kotun irin kwayar da mijin nata ke amfani da shi kafin ya kwanta da ita.
Alkarin kotun Ayodele Omotola bayan da ya gama sauraren su ya daga karan zuwa 23 ga watan Agusta sannan ya shawarce da da su zauna lafiya kafin wannan lokacin da zai yanke hukunci.