Mace Me Kamar Maza: Kalli Bidiyon Yadda Budurwa Ta Yiwa Saurayinta Duka A Bainar Jama’a
Wani bidiyon budurwa ya zagaye duniyar soshiyal midiya wanda aka dauke ta tana yiwa saurayinta dukan raba ni da yaro a cikin mutane a idon mutane. A wannan faifan bidiyo da yake yawo a shafukan sada zumunta an nuno wannan budurwa tana dukan wannan saurayi nata.
A cikin mutane har wasu dsga ciki suka zo domin raba wannan fada amma wannan budurwa ta danne wannan saurayi bata da alamun kyale shi. Wannan bidiyo mutane sun yada shine ta dalilin mamakin da suke, budurwa ta duka saurayi ba saurayi ya duka budurwa ba.
Sannan wannan bidiyo ya nuna saurayin yafi budurwar kaurin jiki amma duk da hakan bai saka ya samu sauki ba a wajen dukan sa da take ko kuma yayi kokarin mayar da martani. Saidai ya tsaya tamkar mahaifiya tana dukan yaron ta.
Mazaje da yawa sun nuna bakin cikinsu da kuma fadin maganganu kan wannan saurayi da ya tsaya budurwarsa tana dukkansa. Wasu mata sun bayyana ko menene yayi mata bai cancanci tayi masa haka ba a cikin mutane a matsayinsa na namiji, wasu daga cikin su kuwa sun nuna farin ciki da faruwar haka har dariya suke.