Kalli Abinda Daukar Namiji Aikin Gida Ya Jawowa Matar Aure Tana Bacci Lokacin Da Mijinta Bayana Na
Kalli illar daukar namiji a matsayin dan aikin gidan, mutane sun bayyana wani bdiyo a matsayin darasi ga masu daukar mazaje a matsayin masu aikin gidansu kamar shara, wanki, wanke wanke, wasu ma harda dafa abinci maza ke yi matan su basu iyawa.
Mun samu wannan bidiyo ne a shafin sada zumunta wato (Facebook) wannan bidiyo ya samu dubbanin masu kallo. Sannan wannan bidiyo ya janyowa masu daukar maza a matsayin masu aiki zagi da kananun maganganu.
A wannan bidiyo an nuna wani namiji kusan dan kimanin shekaru 40 ya shiga dakin matar gidan zaiyi shara ko muce muffin, yana shiga ya tarar da matar gidan tana bacci a saman gado. Tana sanye da wata karamar rigar bacci saita daura zani saboda kusan dai yadda rigar bacci take.
Yana shiga tayi bacci sosai wannan zani data daura sai ya dan yaye kadan ana ganin cinyoyinta hakan ne ya dauki hankalin wannan dan aiki, ya fara kai hannunsa zai karasa cire zaini data daura din dukka, ya kai hannunsa sau da yawa amma yana tsoro.
Daga karshe ya cire tsoro yana fara cire wannan zani matar baccinta baiyi nisa ba sai taji tayi sauri ta tashi domin taga wanene, sai taga wannan dan aiki ne yayi ta kokarin bata hakuri. Amma ta nuna masa babu wannan maganar shiba mutumin arziki Bane.