News

Subahanallahi! Kalli Sabon Salon Lalacewar Tarbiyya Samari Da Yan Mata

Abu ne sananne a wurin dukkanin musulmi dama wadanda ba musulmi ba cewa addinin musulunci ya bada cikakkiyar kulawa a bangaren tarbiyya, idan kace gabadaya addinin musulunci sunansa tarbiyya bakayi kuskure ba.

ALLAH subhanahu wataala ya aiko annabawa daban daban ga alumma daban daban duk domin tabbatar da ko kuma gyaran tarbiyya, hakan yasa aka saukar da littattafai da dama, kamar su attaura da injila da zabura da kuma alqurani mai girma, kuma aka ware malaika guda wanda aukinsa kawai saukar da wahayi ga annbawa, duka dai domin tabbatar da ko kuma gyaran tarbiyya.

Idan muka koma baya, wato asali ko kuma ince tushe,yadda zamuga ALLAH subhanahu wataala ya shirya tsarin tarbiyya ga fiyayyan halitta annabinmu Muhammad saw, ta yadda aka haifeshi maraya, ba uba kuma mahaifiyar sa bata wuce shekara shida ba ta koma ga, ALLAH, hakan yasa ya taso hannun dangi cikin kyakkyawar kulawa da tausayawa, malamai sunce anyi haka ne domin a nuna mana yadda ake hada karfi da karfe wajan tarbiyya.

Bayan ya girma ALLAH ya zaba masa mata ta gari, da abokanai na gari, domin samun wadannan jinsi biyu managar ta, wato mace ta gari fa aboki na gari na taimakawa wa wajan samun ingattacciyar tarbiyya.

Musulunci ya wajabta tarbiyya, kuma ya fadi wadanda tarbiyya ta wajaba akansu, kuma ya koyar da su yadda zasu tarbiyyantar da wadanda aka daura musu hakkin. Tarbiyyan tarwa.

Gyaruwa ko lalacewar tarbiyya tana kan jinsin mutane uku 3 na farko iyaye, na biyu makaranta, na uku muatanan unguwa, idan wadannan turaku uku sukayi tsayiwa irinta daka, bisa kyakyawar niyya kowa ya sauke bakin gwargwadon nauyin da ke kansa na tarbiyya to babu maganar lalacewar tarbiyya awannan al umma, idan aka samu akasin haka kuwa to sai dai ace inna lillahi wa inna ialihi rajiun.

Nauyin dake kan uwa da uba dangane da tarbiyya.

iyaye sune dirka ta farko da hakkin bada tarbiyyar ƴaƴa ta hau kansu, shiyasa manzon Allah saw yace (kowanne abun haihuwa ana haifarsa ne akan fidrah ta addinin musulunci , sai daga baya iyayansa su maidashi bayahude ko kirister ko kuma bamaguje ) da wannaan zamu fahimci cewa lallai iyaye suke kan gaba da kaso mafi tsoka wajan gina tarbiyya ko rugujewar ta.

Mafiya yawan lokutan yara suna yin sane agida tare da iyaye, musanman ma uwa mace don haka ya zama wajibi gareta tayi aiki tukuru wajan sauke nauyin da allah ya dora mata na tarbiyyar yayanta kamar yadda shima uba ya zama tilas ya sauke nasa nauyin.

Nauyin da ke kan makaranta, lallai makaranta itace ta dirka ta biyu wajen tabbatar da ingattacciyar tarbiyya yara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button