Rayuwa Kenan! Duniya Ba Wajen Zama Ba
Wani mutum mai shekaru 36 da haihuwa da aka bayyana sunansa da Owolabi Musiliu ya shiga komar ‘yan sandan jihar Ogun bisa zarginsa da kashe budurwarsa, Fausat Idowu.
Musiliu, wanda bakanike ne ya dauki budurwarsa Fausat mai shekaru 40 da haihuwa zuwa otal a Abeokuta don su biya bukatar juna, kawai sai Fausat wacce bazawara ce mai ‘ya’ya 4 ta kama rashin lafiya kuma kan kace me, ta sheka barzahu.
A jawabi Musiliu da ya gabatar ga manema labarai a lokacin da kwamishina ‘yan sandan jihar Ogun, Ahmed Iliyasu ya yi holinsa a jiya Juma’a ya bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da shi da budurwasa mai rasuwa suka nemi da su biya bukatar junansu tun bayan da suka fara soyayya wata shida da suka wuce.
Musiliu wanda ya ke da aure har da ‘ya’ya 4 ya ci gaba da cewa sun fara cire tufafinsu don su fara abinda ya kawo su otel din ne fa sai jikin Fausat ya fara daukar zafi, daga nan kuma sai ta fadi kasa wanwar, lamarin da ya gaggauta daukarta don ya kaita asibiti, inda a kan hanyarsa ta zuwa asibitin ne ta rasu.
A nasa jawabin, kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana cewa Musiliu bai sanar da ‘yan sanda batun mutuwar Fausat a hannunsa ba kuma bai sanar da ‘yan uwanta ba, kawai sai ya yi gaban kansa ya haka wani kabari mara tsawo ya binne gawar Fausat a kusa da gidanta da ke kan titin Abeokuta zuwa Ibadan
Kwamishina ‘yan sandan ya ci gaba da cewa bayan ‘yan sanda sun kama Musiliu ne sai ya kai su inda ya binne gawar Fausat tare da bayyana musu cewa tsoro ne ya hana shi ya yi rahoto ga ‘yan sanda ko ya fada wa ‘yan uwanta, inda ya boye gawar zuwa dare ya kuma binneta a wani kango.
Kwamishina Iliyasu ya bayyana cewa kanin mai rasuwa Fausat ne ya yi rahoto ga ‘yan sanda kan batar ‘yar uwarsa a ranar 1 ga watan Fabrairu wacce ta fita don halartar bikin radin suna a unguwar Bode Olude.