Wannan Ce Rawar Da Yan Mata Sukayi A Gidan Gala Wanda Ta Jawowa Hausawa Zagi
A yau muke samun rahoto kan wasu yaran hausawa mata wanda suka je gidan gala suna tikar rawar da mutane suka fassara ta da rashin kunya da tarbiya.
Mutane sun koka kan yadda yazun samari da yan matan hausawa suke zubar masu da mutuncin addini da al’ada.
Sunyi wannan magana ne domin duk inda kaga musulmi kuma bahaushe zaka ga asalin kamala da nutsuwa a tattare gashi dalili kuwa shine da addininsa da al’adarsa suna kamanceceniya wajen dokokin zamantakewar rayuwa cikin kamata da dacewa da kamun kai wannan da nisantar abun kunya.
Wannan dalili ne yasa bidiyon wannan matan hausawa da suke rawar da mutane hausawa suka kalle ta a matsayin rashin kunya da tarbiya sannan domin ya sabawa koyawar addininsu da al’adarsu sannan sun janyo wadanda ba hausawa ba suna fadin abubuwan da basu kamata ba saboda wannan bidiyon.
Idan baku manta ba a kwanakin nan manyan yan cikin gwamnati sun fara saka baki da mayar da hankali kan irin rashin tarbiyar da yaran hausawan suke a shafukan sada zumunta har gwamnati ta fara sakawa ana kama su domin suna zubar masu da mutunci sannan suna bata tarbiyar wanda suka taso da tarbiya a gidansu.
Wannan shine bidiyon wadannan matan a gidan gala