News

Cikin Dare Na Dauka Matata Ce Shiyasa Na Dirkawa ‘Yata Ciki

Jami’an ƴan sanda sun cafke wani mutum mai suna Mfon Jeremiah, mai shekaru 39 da ya ɗirkawa ƴarsa mai shekaru 13 ciki a jihar Ogun.

Lamarin ya faru ne bayan matar Jeremiah ta kai mijin nata ƙara wajen ƴan sanda, inda ta bayya cewar ta ga ɗiyarta da ciki kuma da ta tambaye ta tace mahaifinta ne ya yi mata.

Yayin da ƴan sanda ke bincike an kai yarinyar asibiti inda likita ya tabbatar tana ɗauke da ciki wata 4.

Kazalika Jeremiah ya amsa laifinsa, sai dai ya bayyana cewar ya zaci da matarsa yake jíma’i a lokacin da yake saduwa da ƴar tasa.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar SP Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ana kan bincike.

Kuce gaba da bibiyar wannan shafin namu mai al’barka domin samun labarai masu ingance akoda yaushe mungode da ziyarar wanna shafin namu mai Albarka na.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button