News

An Kama Likitan Da Yake Lalata Da Yan Mata Marasa Lafiya A Cikin Ofishinsa

‘Yan sanda a Nijeriya sun kama wani likita da ake zargin yana yi wa ‘yan mata ciki, yana sayar da jariransu.

‘Yan sanda sun ce sun samu wasu ‘yan mata biyar masu ciki, wadanda shekarunsu suka kama daga sha biyu zuwa sha bakwai, a asibitin likitan dake garin Enugu, a sashen kudu maso gabashin kasar.

‘Yan sanda sun ce mutumin ya amsa cewar shi ke yi wa ‘yan matan ciki, yana sayar da jariransu, sun kuma ce zasu gurfanar da shi a gaban kotu.

Matsalar fataucin yara , matsala ce da ta yi kamari a Nijeriya, inda aka sayar da yara domin su rika aikatau, ko kuma karuwanci.

Wani labari wanda jaridar Premium Times Hausa ta rawaito ya tabbatar da cewa rundunar ƴan sandan jihar Legas ta kama shahararren likitan cutar daji Femi Olaleye da laifin yi wa ‘yar uwan matarsa fyade.

Olaleye wanda shine mai mallakin asibitin kula da masu fama da cutar daji ‘Optimal Care Centre’ dake Surulere a jihar Legas ya yi shekara daya da watanni 9 yana lalata da ‘yar uwar matarsa.

Uwargidan likitan Remi Olaleye wacce ita ce ta kai karar sa kotu ta ce ya ci mutuncin ta matuka.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Benjamin Hundeyin ya ce rundunar ta aika da file din karar likitan zuwa fannin dake gurfanar da masu aikata laifi irin haka domin gudanar da bincike da shawara.

Likitan ya ki amsa kira da sakonnin tes da aka aika wayoyinsa kan zargin fyade da ake masa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button