News

Abinda Tsohon Sarkin Kano Sunusi Khalifan Tijjaniya Na Kasa Yayi Ya Jawo Masa Magana

Kada mu zama wakilan kare son zuciyarmu don Allah. Duk da cewa akwai Malamai da sukayi maganganu akan halaccin gaisawa da mace ko rashin halaccinsa akwai abubuwa wanda suka saba da al’adunmu na Hausa Fulani.

Kamata ya yi ‘yan uwa makunsanta Malam Muhammadu Sunusi na II su nusar da shi Illar yin hakan kai ko a al’adancen ne ma da irin nauyin da yake akansa a yanzu sa6anin a baya.

Ba zan manceba akwai shekarun baya da Malam Bala Lau da Kabiru Gombe sukaje birnin London suka sanya kaya ba irin ta Malam bahaushe ba, waďannda suka sa6a da al’adunmu mune sahun farko don yin kwarmato akan abunda suka aikata, bafa wa addini suka sa6aba amma mukaita musu Isgili don sunyi abunda ya saba da al’adarmu sai ďaya daga Jagororinmu da yake amsa sunan Khalifa na Shehu Ibrahim Inyass (R.A) ya riqa gaisawa da Mata sai muja baki muyi shiru gaskiya hakan kin gaskiya ne karara da yin kwaskwarima wa lamarin..

Lalle ina kira ga ‘yan uwa makusanta Malam Muhammadu Sunusi da su duba yiwuwar nusar da Sarki illar wannan lamari a al’ardarmu da gaisawa da macen da ba muharramarka ba, hakan shine yafi dacewa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button