Innalillahi Kalli Abinda Tura Yan Mata Talla Ya Jawo
Talla wata a’lada ce da ake dora wa kananan yara – mata da maza – abubuwan sayarwa domin su rika yawo kwararo-kwararo suna sayarwa da zummar samun abin sanya wa a bakin salatin iyayensu.
A wannan makon, mun mayar da hankali ne kan yadda ake dora wa kananan yara mata talla da kuma illar da hakan kan haifar.
Kananan yaran da shekarunsu suka kama daga biyar sukan dauki tallan abinci da abin sha inda suke tafiya kasuwa da wuraren taruwar jama’a domin sayarwa.
Hakan yakan karfafa gwiwar iyayensu su ci gaba da dora musu talla da zummar samun kudin yin kayan daki idan lkacin auren yarinyar ya zo.
Iyayen sun yi amannar cewa tara irin wadannan kudade da aka samu daga talla na taimaka musu wajen fita kunya loakcin auren yaran. Shi hakan gaskiya ne?
Ko dai wata dabara ce da iyayen ke amfani da ita wurin ajiye nauyin da ya rataya a wuyansu na ciyar da kuma tufatar da ‘ya’yansu musamman mata?
Ko da a cikin dabbobi, babban nauyin da ya rataya a wuyan iyaye shi ne kula da ‘ya’yansu.
Don haka nauyin da ke wuyan iyaye shi ne kula da ‘ya’yansu. Amma me ya sa iyayen wadannan ‘yan mata da ke tallace-tallace suke yin watsi da wannan nauyi?
Wasu na da ra’ayin cewa hakan na faruwa ne saboda talauci. Sai dai wasu na sukar iyayen da cewa sakaci da rashin son daukar nauyin iyalansu ne kawai ke haddasa tallace-tallace.
Kazalika wasu na ganin laifin al’uma da gwamnati ne, wacce alhakin kula da jama’a ya rataya a wuyanta.
Koma dai mene ne, abin da ya fito fili shi ne yawon tallace-tallace a wurin ‘ya’ya mata, har ma da mazan, yana jefa su cikin hadarin fuskantar fyade da musgunawa da ma sace su.
Don haka mece ce makomar wadannan yara da ke gararamba a titi maimakon zuwa makaranta?