News

Yadda Aka Kamashi Yana Lalata Rayuwar Budurwa

Wannan wani matashi ne wanda ke bayyani da kansa da Yadda yayiwa mata fyade sosai wanda yace yayiwa mata alaka 40 wanda kuma yace a wannan shekara ne ya fara A’uzubillahi.

Tabbas wannan mutum yayi aika aika sosai a cikin wannan al’amari Allah ka yafemana amen.

Kamar yadda ta bayyana a wani bidiyo wanda Rigar ‘yanci ta wallafa a shafinta na YouTube, shekarunta 20 da haihuwa kuma ta kwashe shekaru 7 su na soyayya da matashin har maganar aure ta shiga tsakaninsu.
Ta ce mahaifiyarta ta rasu kuma mahaifinta ba ya da lafiya, wannan yasa ta bayyana kanta gaban kungiyar tana neman a taimaka a kwato mata hakkinta.

A cewarta, matashin ya kawo kayan aurensa wanda daga bisani ya aika aka amsar masa bayan ya tilasta mata yin lalata da shi.

Ta ce ya fito mata adda ne inda yace matukar bata amince da shi ba sai ya yanka ta, wanda hakan yasa bisa dole ta yarda da bukatarsa.

Daga bisani ta gane cewa ta dauki juna biyu, wanda tayi gaggawar sanar da shi. Sai dai ya amso mata wasu magunguna daga hannun wani likita na zubar da ciki.

Ta shaida yadda bayan ta sha su cikin yaki zubewa wanda hakan yasa ta nufi asibiti tare da ‘yar uwarta inda aka tabbatar mata da cewa tana dauke da ciki.

Bayan ganin hakan ne ya shaida wa iyayensa cewa ya fara ganin sauyi tattare da ita wanda yasa yake so a amso masa kayan aurensa daga gidansu Fatima.

Wannan lamari ya yi matukar tayar musu da hankali, hakan yasa su ka bayyana gaban kungiyar kwatar hakki don a amsar musu hakkinsu ita da yayarta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button