Kalli Yadda Dan Sanda Ya Dawo Gida Ya Kama Matarsa Da Kwarto Tana Cin Amanarsa
Matsalar latata tsakanin daliban manyan makarantun gaba da sakandare ya addabi manyan makarantun kasar nan a ‘yan kwanakin nan.
Wanda aka yi ba da dadewa ba kuwa shine na jami’ar Babcock, wanda aka gano bidiyon wata budurwa suna lalata da saurayi.
Babu jimawa kuwa, hukumar jami’ar ta fatattaki dalibar.
Hakan kuwa ya jawo cece-kuce daga wajen mutane da dama. Wasu na ganin anyi dai-dai da aka kori dalibar inda wasu ke ganin akasin hakan.
Wasu na kafa hujjar cewa, lamarin bai faru a cikin makarantar ba, don haka hukumar makarantar bata da hurumin katsalandan ga rayuwar dalibar.
Amma sai dai kash! Sun manta cewa, shaidar digirin ana bada ita ne saboda kyakkyawar dabi’a da kuma ilimi.
Duk inda aka rasa dabi’a ta gari, toh kuwa ilimin na iya samun babbar nakasa.
Kwatsam kuma sai labarin wasu dalibai biyu da folitaknik din jihar Edo ta kora ya mamaye kanun labarai.
Su kuwa daliban an koresu daga makarantar ne sakamakon kamasu da aka yi suna lalata a cikin dakin karatu.
Takardar da makarantar ta fitar da ke bayyana korar daliban, ta nuna cewa an kamasu dumu-dumu a dakin karatu suna aikata badalar.