News

Innalillahi Kalli Irin Matsalar Da Shaye Shaye Ta Jefa Ƴan Mata Da Samarin Wannan Zamani

A duk duniya a yau, babu inda ya kai arewacin Najeriya musamman jihar Kano, yawan masu shan Codeine, wani maganin tari mai sanya mutum bacci.

Masu bincike sun tabbatar wannan yana da alaka da halayyar jama’ar Arewa dake haifar wa da ‘yan mata da matan aure damuwa da rashin abin yi.

Matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi da kayan maye ta zama ruwan dare a arewacin Najeriya musamman a jihar Kano.

Bincike ya nuna lallai da yawan masu shan kayan mayen nan suna yi ne don su yaye wa kan su bakin ciki ko damuwa da suke tsintar kan su a ciki.

Sabon salon da ya fito, mata kuma ke yayi, shine shan Codeine da Rafanol da ma Benylin da sauran miyagun kwayoyi.

Abin tada hankali shi ne yadda ‘yan mata suke shiga irin wannan mummunar dabi’a. Tun daga fatauci da sayarwa har zuwa shaye-shayen miyagun kwayoyin.

Yin hakan ba karamar illa yake ga jikin dan adam ba, yana lalata hanta da koda a jikin mutum har ya kai ga rayuwar mutum ta salwanta.

Da yawan mata suna shiga wannan mummunan dabi’ar ne ko kuma su dinga yawo Otal bin samari, kuma sama da rabin mashayan kwayoyin mata ne.

Wasu kuma da yawan su masu sayan kayan mayaen matan aure ne masu fama da bakin cikin zamantakewar aure, suna shan kwayoyin ne saboda su dauke hankalinsu daga damuwar da suke ciki.

Da yawan su suna shan Codeine dinne saboda ya yaye musu bakin ciki da damuwa, yadda wata matar ta shaidawa gidan jaridar BBC ta fara sha ne bayan mutuwar aurenta.

Wasu kuma ‘yan matan suna shan kwayoyin ne saboda su yaye wa kan su damuwa, wata da aka gana da ita ta shaida cewa tana shan kwayar ne domin ta yaye bakin cikin da ta shiga saboda saurayinta ya rabu da ita.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button